Watan Azumin tsofaffi tsakanin Bidi'a da sunnah 1.
Hakika ubangiji ya aikomana manzo yakuma alakanta shiryuwarmu ga yimasa da'a da biyayya tare da wajabta mana kwaikwayo dashi matukar dagaske tsira muke so..
Baya ga haka sai yazama sharadin karbuwar aiki agun ubanji sai yazama akwai Ikhlasi aciki tare da kasantuwar aikin bisa koyarwa ta ma'aiki (s.a.w). Sai yazama duk kyawun aikinka ahangenka da tunaninka matukar yarasa daya cikin biyunnan damuka ambata ba mai kyaubane amahanga ta shari'a domin addini ba dan ganin dama bane...
Hakika ansamu hadisai masu yawa dasuke kunshe da falaloli namusamman da Ibadu awatan Rajab wanda suke kodai Raunane kokuma nakarya ko kuma basu kebanci watan da falalar kararaba, shi kwa addini ba a gina shi akan haka.
Malam Ibn Hajar yace:
لم يرد في فضل شهر رجب ولا في صيامه ولا في صيام سيئ منه معين ،ولا في قيام ليلة مخصوصة فيه حديث يصلح للحجة.
Ma'ana: babu wani hadisi daza'a iya kafa hujja dashi dayazo gameda falalar watan Rajab , hakanan ware wasu ranaku dan azumtarsu cikinsa shi kadai, hakanan kebantar wasu darare dan yin tsayuwar dare cikinsu.
Duba: Tabyinul Ajab, shafi na 5-6.
Abunda ya inganta game da watan Rajab.
Ubangiji madaukakin sarki ya ambata awatannin shekara guda 12 akwai guda hudu masu alfarma, kamar yanda yafada acikin Taubah
"إن عدة الشهور عند الله اثنا عشر شهرا في كتاب الله يوم خلق السموات والأرض منها أربعة حرم"
manzon Allah s.a.w ya ambata wadannan watanni masu alfarma guda hudu kamar yanda yazo cikin hadisin Abu Bakrata wanda Bukhari da muslim suka rawaito
السنة اثنا عشر شهرا منها أربعة حرم،ثلاثة متواليات ذو القعدة وذوا الحجة والمحرم ورجب مضر الذي بين جمادي وشعبان
Ma'ana: "shekara wata 12 ce, acikinta kuma akwai watanni hudu masu alfarma, uku cikin watannin ajere suke, -sune-: zhul qa'adah da zhul hijjah da Muharram dakuma Rajabu mudar wanda ke tsakanin Jumada- jumadal akirah- da sha'aban".
Acikin hadisin sai ya ambaci watan Rajab acikin watanni hudun masu alfarmar
Zamu cigaba